A song made by maman Annour
A song made by maman Annour
Wallahi! Bikin Fatima! Kai! Masha Allah!
Da sunan Sarkina, Allah shi daya ke bani
Ga waka yau ta biki, Fatima naimiki ba raini
Kikama mijinki da kyau, Fatima ina karayin tini
Fatima kinfisu kyau da ado, ba'a magana iye!
Aure Andaura, dangi kowa na murna!
Fatima ce Amarya, munzo muyi murna, iye!
Kowa na farin ciki, ba mai gajiya!
Fatima, Allah ya sanya alkhairi, iye!
Biki yau yayi biki, dangi kowa na murna
Na hangi iyayenki sunzo suma sun murna
Na hangi kawayenki sunzo suma sun murna
Fatima taci ado lallai, aure andaura, iye!
Aure Andaura, dangi kowa na murna!
Fatima ce Amarya, munzo muyi murna, iye!
Kowa na farin ciki, ba mai gajiya!
Fatima, Allah ya sanya alkhairi, iye!
Ki ladabi a gare shi, Fatima karkiyi jayayya
Komai in ya ce yi, Fatima tashi kidau niyya
Aure ya dauru, Fatima sai kiyi dariya
Lallai kun dace ke da mijinki, agaisheki iye!
Yayye na murna, Lubabatu na murna, Hauwa da Halimatu na murna!
Nana tana murna, Yaya Basiru yana murna!
Auwalu da Abdulrahaman, Amina, Zainab ma na murna!
Bishir ma na murna, Umar, Mustapha, kowa na murna!
Aure Andaura! Dangi kowa na murna! Fatima Amarya! Masha Allah!