A song made by GMS AI Photo Design
A song made by GMS AI Photo Design
Sadiya mutanan sudan, wakar biki ta sauka, matar Alhaji dan baba mai goron dai. Hajiya ayya dai... Caucaucau
Ya ilahu sarki Allah kaike ban ruwa da abinci
Nai niya ayau zan wakar sudan kasa ta karamci
Naga dubu dubu sun taru sabon kidanmu mai hana bacci
Ga shugabarmu nan ta hadin kai.
Sadiya da bata sankai.
Tafi muje kawai je sakai.
Du wanda zaya tareki ni zanbuga mai kulki.
Sadiya mutanan sudan taronki yau ya taru
Du wanda zai tada shi barni inhada shi dagaru
Marga marga babban dutse sai dai tabaki bakya turu
Zinariya adon dawisu.
Kinsha gabasu kinzartasu.
Dole su soki ko sunki kansu.
Rabbanu yaja kwananki gamu muntawo shagalinki
Yau baitikan ba sulhu saidai kuji ku kauda idanu
Saika kai akema waka inbaka kaiba saidai sannu
Sadiya ko ta isa takai sahun giwa kin zarce na shanu
Yau bikin kine ba waiba.
Karki ce bakya taka ba.
Mu awajanmu kece babbba.
Domin kina hada kanmu bakya fushi da saurin tsaki
Sadiya mutanan sudan taronki yau ya taru
Du wanda zai tada shi barni inhada shi dagaru
Marga marga babban dutse sai dai tabaki bakya turu
Zinariya adon dawisu.
Kinsha gabasu kinzartasu.
Dole su soki ko sunki kansu.
Rabbanu yaja kwananki gamu muntawo shagalinki
Ansha tabaki danki fusata amma kishanye fushinki
Fada da aljani ba dadi nan za,aganki dole abarki
Kinsha tabara kinsha yasin karyar munafiki ya tareki
Ku ban waje na gaida ubana dan bazanki mai baiti ba
Dan Baba mai goron dai waya ce dakai ba kai ba
Me kyautar da ke hana bacci waye cikin mu bai samu ba
Me gida ga Allan guguro
Me gida ga ali da abubakar
Me gidan abubakari da ubaliyo
Nayima baitinka na sadiya agaida saraki...
Lantana matso ga baiti jinjina ga babbargiwa
sun buga dake sun barki saida kika sasu gudawa
Wai ina ko dije taboye jinjina ga yayar Aunty
Yaya ga ummi uwar gida a gun sani baban lado
Hauwa ta dan dala mai goro aminiya ga hafsa gajera
Matso tawo kixo ga baiti du mekinki yayi asara
Wai ina su ramla su taso dan bikinfa bai kare ba
Kanwa ga lantana ga baiti inkin shuru bazan kara ba
Hauwa ta dan baba mai gonar nama matso ga baiti
Hajja riha uwar gidan maharazu nakaki
Gambo uwar dan gurgu naga kina rawa hada juyi
Wai ina mutanan toci masu kaunar mutum dan Allah
Kaso a soka shine so mutanan toci na gaida ku
Hauwa da abu mutanan toki ku marmatso ga bati
Da marya da hanne uwar yan yaran naga masu basira
Kuna rawa kuna juya banga kuna zubar da dala ba
Abbarka yar toki tanayin rawa tana juyawa
Sainasa matanan hasahisa rahine na gaida ki